Amurka-Faransa

Kotun Amurka zata yanke wa strauss-Khan Hukunci

Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn a lokacin da yake gabatar da Jawabi akan makomar tattalin arzikin Duniya a birnin Kiev
Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn a lokacin da yake gabatar da Jawabi akan makomar tattalin arzikin Duniya a birnin Kiev Reuters/Gleb Garanich

A ranar Juma’a mai zuwa ne alkalin da ke shari’ar zargin yunkurin fyade da ake wa Tsohon shugaban Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, Dominique Strauss Kahn, zai yanke hukunci a birnin New York.Lauyan Strauss Kahn ya bukaci alkali Douglas McKeon da ya yi watsi da zargin da Nafissatou Diallo ta gabatar akansa, saboda lokacin da aka zarge shi da aikata laifin, yana da kariyar diflomasiya.

Talla

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.