Colombia-France-journaliste-FARC

Alamu na nuna cewa, kungiyar yan awaren FARC a kasar Colombia ce, ta sace dan jaridar nan na tashar TV din France24.

France 24 journalist Roméo Langlois
France 24 journalist Roméo Langlois France 24

Romeo Langlois, dan jaridar nan dan kasar Fransa na rike ne ga hannun kungiyar yan awaren FARC a kasar ta Colombia. In ji shugaban kasar Colombia Juan Mannuel Santos, wanda ya nemi kungiyar ta FARC ta sako dan jaridar dake yi wa tashar TV ta France 24 aiki.Shi dai Romeo Langlois ya yi batan dabo ne, a ranar assabar 28 da watan Aprilun da ya gabata, bayan wata taho mugamar da aka yi tsakanin dakarun gwamnatin kasar, da na mayakan sunkurun kungiyar FARC a Colombia.