Pakistan-Amurka-Afghanistan

An cika shekara da kisan Osama, Obama ya yi kiran sansatawa da Taliban

Marigayi Osama Bin Laden Shugaban kungiyar al-Qaeda da wanda ya gaje shi Aymar Zawahiri
Marigayi Osama Bin Laden Shugaban kungiyar al-Qaeda da wanda ya gaje shi Aymar Zawahiri

A rana irin ta yau ce dakarun Amurka suka ce sun kashe Osama bin Laden a Pakistan, amma kuma shugaban Amurka Barrack Obama ya yi kiran zama teburin sasantawa da Taliban a wata ziyarar bazata da ya kai a Afghanistan.

Talla

A lokacin da Obama ke gabatar da Jawabi a bukin cika shekara da kisan Osama, shugaban ya yi kira ga kungiyar Taliban ta katse hulda da Al Qaeda domin cim ma zaman Lafiya.

A ranar 2 ga watan Mayu ne dakarun Amurka suka ce sun kashe Osama bayan kai wani samame a wani gida da yake buya a yankin Abbottabad kasar Pakistan.

A yau Laraba Gwamnatin Pakistan ta bayyana fargaba game da yiyuwar kungiyar Al Qaeda zata kaddamar da hare hare domin nuna bakin-cikin mutuwar Shugabanta.

Kashe Osama da dakarun Amurka suka yi a Pakistan ya haifar da kiyayya tsakanin kasashen Biyu domin Amurka ta zargi Pakistan matsayin mafakar ‘yan kungiyar Al Qaeda.

Ana sa ran Ayman al-Zawahiri, wanda ya gaji Osama matsayin shugaban Al Qaeda zai kai ziyara Pakistan tare da shugaban Taliban Mullah Umar.

A jiya Talata ne Shugaban Amurka, Barack Obama, ya kai wata ziyarar bazata kasar Afghanistan, inda ya sanya hannu akan yarjejeniyar shekaru 10 kan rawar da Amurka zata taka, bayan kawo karshen aikin dakarunta a shekarar 2014.

Ziyarar tasa ta yi dai dai da cika shekara guda da halalaka Osama bin Laden, amma shugaba Hameed Karzai yace, yarjejeniyar zata daidaita Amurka da Afghanistan domin aiki tare.

Bayan ziyarar Obama a Afghanistan, wasu jerin bama bamai sun tashi a Kabul wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane Bakwai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.