Rasha

Sozojin Rasha biyar sun rasa rayukansu a cikin wani hadarin fashewar Nakiya a yau.

wasu matasan daga sozojin kasar rasha
wasu matasan daga sozojin kasar rasha RFI/Keo Chhaya

Sojan kasar Russia 5 ne suka gamu da ajalinsu a yau laraba sakamakon tarwatsewar nakiya, a wani wuri da Sojan kasar ke koyon harbi, a tsakiyar kasarMa’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa, nakiyan ta tarwatse ne a lokacin da sojojin ke sauke wasu nakiyoyi daga cikin mota, da ake ganin wadannan nakiyoyi sun daina aiki.Sanarwan na cewa, akwai wasu sojan 3 da suka samu raunuka.