China-Amurka

China tace Chen zai iya neman izinin karatu a kasashen Waje

Chen Guangcheng tare da Jekdadan Amurka a China Gary Locke
Chen Guangcheng tare da Jekdadan Amurka a China Gary Locke REUTERS/US Embassy Beijing

Gwamnatin kasar China tace Makaho dan rajin kare hakkin Bil’adama, Chen Guangcheng, zai iya neman izinin karatu a kasashen waje, a wani mataki na bude kofar kawo karshen sabanin da aka samu bayan ya tsere zuwa Ofishin jekadancin Amurka.

Talla

An kargame Mista Chen ne a wani gida kafin ya tsere zuwa Ofishin Jekadancin Amurka

Wannan na matakin na zuwa ne bayan Mista Chen yace rayuwar shi tana cikin hadari.
Wani da ke wa gwamnatin kasar China bore yace hukumomin birnin Washington sun yi babban kuskure, da suka bari makaho, dan rajin kare hakkin dan Adam Chen Guangcheng ya fice daga ofishin jakadancin Amurka a birnin Beijing.

A zantawar Wei Jingsheng da kamfanin dillacin labarun kasar Faransa AFP ta wayar Salula, yace hukumomin birnin Beijing ba za su bari Chen Guangcheng ya sake ficewa daga kasar ba.

Wei, wanda shi kan shi yake gudun hijira a Amurka tun shekarar 1997, bayan ya shafe kusan shekaru 20 a gidan yarin kasar Sin, yace bai kamata hukumomin Birni Washington su yi saurin amincewa da gwamnatin kasar Sin ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.