Zaben Faransa

Shugabannin kasashen duniya sun taya Hollande Murnar lashe zaben Faransa

François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa wanda ya kada Nicolas Sarkozy
François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa wanda ya kada Nicolas Sarkozy

Shugabannin kasashen duniya da na Turai sun mika sakon taya murna ga Francois Hollande wanda ya lashe zaben shugaban kasar Faransa bayan ya kada Nicolas Sarkozy a zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu.

Talla

Shugaban Gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Jose Manuel Barroso bayan mika sakon taya murnar shi ga Francois Hollande, kuma ya yi alkawarin aiki tare da shi don bunkasa tattalin arzikin Turai.

Fira Ministan Britaniya, David Cameron, ya kira sabon shugaban ta waya, inda ya taya shi murnar nasara da ya samu kan Sarkozy, kamar yadda Fira Ministan kasar Belguim, Elio Di Rupo, ya yi.

A nasa bangaren Shugaba Barack Obama na Amurka, ya taya zababben shugaban murna, tare da gayyatar shi zuwa fadar White House a cikin watan nan, a tattaunawar su ta waya.

A nata bangaren shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta mika sakon taya murna ga Francois Hollande, inda take cewa zata hada kai da sabon shugaban wajen tsara yadda kasashen Turai zasu ci gaba, tare da watsi da zargin cewa nasarar Hollande zata karya dangantakar Jamus da Faransa.

Shugabanin kasashen Latin Amurka da dama, da suka hada da Colombia, Cuba, Brazil da Canada, sun aika da sakon taya murnarsu ga Francois Hollande bisa gagarumar nasarar day a samu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.