Amurka-Faransa

Rikicin Duniya: Sarkozy ya bi sahun Berlusconi, ko Obama zai kai labari?

Shugaban Amurka Barack Obama a yakin neman zaben shi Viginia
Shugaban Amurka Barack Obama a yakin neman zaben shi Viginia REUTERS

A ranar 6 ga watan Mayu ne Nicolas Sarkozy daya daga cikin aminan Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sha kaye a zaben Shugaban kasa bayan Faransawa sun juya masa baya inda suka zabi dan ra’ayin gurguzu, Francois Hollande matsayin sabon shugabansu.

Talla

A ranar Lahadi dai Sarkozy ya bi sahun shugabannin da rikicin duniya ya yi awon gaba dasu, irinsu Gordon Brawn na Birtaniya da Papandreou na Girka da Silvio Berlusconi na Italia da Brian Cowen na Ireland da shugabannin kasar Denmark. Kuma yanzu al’amarin  ke barazana ga shugabannin kasar Spain da Portugal da Shugaban Amurka Barack Obama.

Kodayake awon gaba da shugabannin ya biyo bayan rikicin kasashen su ne bayan kasa magance matsalar tattalin arziki da ya samo tushe tun a shekarar 1930.

Sarkozy na Faransa da Obama na Amurka da Cameron na Birtaniya sun taka muhimiyyar rawa ga lamurran siyasar wasu kasashen duniya, musamman zangar-zangar kasashen Larabawa saboda tasirinsu a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

A watan Nuwamba ne Amurkawa zasu kada kuri’ar zaben shugaban kasa inda Obama ke neman a zaben shi wa’adi na biyu.

Sai dai Obama yana fuskantar kalubalen matsalar tattalin arziki da ta yi awon gaba da aminan shi na Turai inda aka fara hasashen Amurkawa suna iya yin waje da shi daga Fadar white House zuwa garin shi a Chicago.

Akwai matsalar rashin aikin yi da ke addabar Amurkawa da Tattalin arzikin kasar da ke tafiyar hawainiya tare da dimbin bashin da ake bin Amurka.

“Yanzu Zabe ya dogara ne akan ci gaban tattalin arziki, da yadda mutane suke kallon ci gaban da aka samu, ko an samu ci gaba ko kuma akasin haka” inji Conley a cibiyar tsare tsare da binciken ci gaban tattalin arzikin kasashen Duniya.

Wani zaben jin ra’ayin jama’a da Jami’ar Washington ta gudanar akan manufofin Siyasa da diflomasiya, sakamakon ya nuna Obama ya samu rinjaye tsakanin shi da Mitt Romney na Jam’iyyar Republican.

Yana da wahala yanzu a iya yin hasashen sakamakon zaben Amurka saboda matsalar tattalin arziki.

Masana Siyasar Duniya sun ce yanzu masu kada kuri’a sukan yi waiwaye ne domin diba ko an samu ci gaba ko akasin haka kafin su kada wa ‘Yan Siyasa kuri’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.