Syria-MDD

Annan yace tsarinsa na zaman Lafiya a Syria shi ne mataki na karshe

Kofi Annan a lokacin da yake jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya game da Syria.
Kofi Annan a lokacin da yake jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya game da Syria. Reuters

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Syria, Kofi Annan, ya shaidawa kwamitin Sulhu cewa, shirinsa na neman zaman lafiya shi ne mataki na karshe don kaucewa yakin basasa a kasar, a yayin da dakarun gwamati ke ci gaba da diran mikiya kan masu zanga zanga, da azabtar da fursunoni.

Talla

Mista Annan yace, ba zasu lamunce da yadda ake ci gaba da tashin hankali da kuma cin zarafn Bil Adama ba.

Sai dai Kofi Annan, wanda ke jawabi a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bai fadi ranar da zai koma birnin Damascus ba.

Annan wanda shi ne Tsohon Sakatare Janar na Majalisar ya je Syria tun farkon fara aikin sasanta rikicin, amma har yanzu bai koma ba.

Yanzu haka dai Mista Annan yace zai fi mayar da hankali ne kan kawo karshen zubar da jini da ake yi a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.