Amurka

Obama ya yi na’am da auren jinsi a Amurka

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS/Larry Downing

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama ya fito karara inda ya bayyana goyan bayan shi ga auren jinsi guda, a dai dai lokacin da Jahar North Carolina ta zama Jiha ta 30 da taki amincewa da auren.

Talla

“‘Yan Luwadi da ‘Yan Madigo suna da ‘Yancin yin aure” inji Obama a lokacin da yake zantawa da kafar yada labaran ABC News.

Kungiyoyin kare hakkin ‘Yan madigo da ‘Yan Luwadi tuni suka jinjinawa shugaban amma ‘yan adawa sun la’anci al’amarin.

“Muna taya ka murna Shugaba saboda ka kafa tarihin zama shugaba na farko da ya amince da auren jinsi a Duniya” inji Rea Carey babbar jami’ar kare hakkin ‘Yan luwadi da ‘Yan Madigo a Amurka.

Batun auren jinsi yana da matukar tasiri a siyasar Amurka, kuma zuwa yanzu Jahohi shida sun amince da auren, da suka hada da Connecticut da Iowa da Massachusetts da New Hampshire da New York da Vermont da Washington.

Mutumin da ake ganin zai yi wa Jam’iyar republican takara, Mitt Romney ya ki bai wa auren jinsi goyan baya.

Ana ganin dai Shugaba Obama ya yi Caca game da amincewa da Auren Jinsi wanda zai iya rage masa farin jinin siyasa a yakin neman zaben shi wa’adi na biyu a watan Nuwamba.

Fira Ministan Australia, Julia Gillard ta tsaya tsayin daka akan la’antar Auren Jinsi inda tace zata kada kuriar kin amincewa da kudirin a gaban Majalisa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.