Amurka

Ana shawarar fara amfani da maganin rigakafin HIV

Magungunan cutar HIV/AIDS
Magungunan cutar HIV/AIDS

MASU kula da lafiya a kasar Amurka suna shawara kan yuwuwar fara amfani da wani magani mai suna Truvada, a matsayin wanda za a yi amfani da shi don rigakafin cutar HIV, maimakon bayar da shi don warkar da wadanda suka kamu da cutar AIDS. Bincike kan maganin da aka wallafa a shekarar 2010, ya nuna maganin ya rage kasadar kamuwa da cutar ga wasu mutane da kashi 73 cikin 100.Sai dai wadanda basu goyon bayan amfani da maganin suna cewa marasa lafiya za su iya kashe kudin da ya kai Dalar Amurka dubu 14 a duk shekara don sayen shi, kuma zai iya sa mutane su dawo da yin jima’I barkatai, da zai iya jefa al’ummar duniya cikin hadari.