Amurka-Faransa-Diflomasiya

Wasu manzannin A mruka 3 sun ziyarci sabon shugaban kasar Fransa a yau juma'a

François Hollande, tare da shugaban kungiyar tarayyar turai  Herman Van Rompuy
François Hollande, tare da shugaban kungiyar tarayyar turai Herman Van Rompuy REUTERS/Fred Dufour/Pool

Wasu manzannin diplomasiyar kasar Amruka guda 3 a yau juma’a sun gana da shugaban kasar Framsa mai jiran garo Francois Hollande a birnin Paris, kafin ziyarar da yake shirin kaiwa a kasar Amruka a moko mai zuwa, inda sabon shugaban na Fransa zai gana da shugaban kasar Amruka Barak Obama.A ranar lahadin da ta gabata ne, a lokacin da ya gabatar masa da sakon taya murnar zabensa kan mukamin shugabancin kasar Fransa, Shugaban kasar ta Amruka Barak Obama ya gayyaci Francois Hollande, da ya ziyarce shi a Amruka, a daidai wannan lokaci da ake shirin gudanar da tarurrukan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki na gungun G8 a Camp David, da kuma na kungiyar tsaro ta Nato a Chikago.