ICC-Congo

ICC ta bukaci sabon sammaci ga shugaban ‘Yan tawayen Congo

Luis Moreno-Ocampo,Mai gabatar kara a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC
Luis Moreno-Ocampo,Mai gabatar kara a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC REUTERS/Ismail Zitouny

Mai Gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifufuka, Luis Moreno Ocampo, ya nemi wani sabon sammacin kama shugaban ‘Yan Tawayen Congo, Janar Bosco Ntaganda, da Sylvester Mudacumura, wadanda suka jagoranci tawayen da aka kashe miliyoyin mutane a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Talla

Tun a shekarar 2006 ake neman Janar Ntaganda, yayin da ake neman Muducumura, saboda jagorancin kungiyar FDLR, da ake zargi da kisa, fyade da cin zarafi da kuma azabtar da jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.