Girka-EU-IMF

Hukumar bayar da Lamani ta Duniya ta bayyana jingine tuntubar juna da kasar Girka

Shugabar hukumar bayar da lamani ta duniya IMF Christine Lagarde
Shugabar hukumar bayar da lamani ta duniya IMF Christine Lagarde REUTERS/China Daily

Asusun bada lamuni na duniya IMF yace zai jingine tuntuba da kasar Girka har sai bayan an yi zabe, duk da cewa za’a kafa Gwamnatin rikon kwarya ne.Mai Magana da yawun Asusun David Hawley ya fadawa manema labarai a Washington na kasar Amirka cewa, anyi la’akari da cewa, an kira zabe a kasar, kuma Asusun zai koma mu’amulla da kasar bayan an kaddamar da Gwamnatin.