Turkiya-Syria-MDD
kasar Turkiya ta roki MDD ta tura masu zura ido dubu 3 a Syriya
Wallafawa ranar:
PM kasar Turkiyya Recep Tayip Erdogan ya roki MDD data ga lallai ta tura wakilai masu sa idanu da suka kai 3,000 zuwa kasar Syria.PM ya gayawa manema labarai a kasar Bulgaria yayi wata ziyara cewa adadin da MDD tace zata tura, wato 300 san basu wadatar ba domin sa idanu a kasar ta Syria.PM yace abin takaici ne yadda har yanzu babu alamun an fara aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Syria.