G8-Amurka-Birtaniya

Shugabannin kasashen G8 sun tattauna ta salula kafin taronsu

Tambarin G8 kasashe Takwas masu karfin tattalin arzikin Duniya
Tambarin G8 kasashe Takwas masu karfin tattalin arzikin Duniya Reuters

Shugabannin Kasashen Turai da ke cikin kungiyar kasashe takwas da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, sun tattauna a tsakaninsu ta wayar salula, kafin taron da zasu yi a Washington.

Talla

Tattaunawar shugabanin na kasashen Jamus, Faransa, Italia da Birtaniya, da kuma shugabanin kungiyar kasashen Turai, ya biyo bayan sukar da David Cameron ya yi, na cewar ko su magance matsalar kudin euro, ko kuma kudin ya rushe.

Kakakin Cameron tace, tattaunawar da shugabanin suka yi na da nasaba da taron G8, da kuma matsalar kasashen Turai, kamar yadda shugaban kungiyar Herman Van Rompuy ya bukata, don daukar matsayi guda.

Fira Ministan Britaniya, David Camern yace Yankin kasashen Turai suna tsaka mai wuya, ganin irin matsalolin tattalin arzikin da ke addabar su, da suka hada da basusuka, da rage darajar bankunan wasu kasashen, inda yake cewa magance matsalar ya zama tilas, ko kuwa Yankin ya shiga mawuyacin hali.

Birtaniya dai bata cikin kasashe 17 masu amfani da kudin na euro.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.