NATO/OTAN

Kungiyar NATO/OTAN na neman hadin kai bayan Faransa tace zata janye dakarunta a Afghanistan

Taron Shugabannin kasashen kungiyar kwancen NATO ko OTAN a Chicago
Taron Shugabannin kasashen kungiyar kwancen NATO ko OTAN a Chicago REUTERS/Yves Herman

Shugabannin kungiyar kawancen tsaron ta NATO ko OTAN sun ce zasu hannunta tafiyar da sha’anin tsaro ga dakarun Afghanistan a tsakiyar 2013 bayan sabon Francois Hollande yace zai fice da dakarun Faransa daga Afghanistan na bada jimawa ba.

Talla

Ana sa ran shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari tare da wasu shugabannin kasashe 30 zasu gana da kasashen kawancen NATO ko OTAN 28 a yau Litinin.

Tun a jiya Lahadi ne kasashen kawancen NATO ko OTAN suka fara gudanar da taro a Chicago akan batun Afghanistan.

A yau Litinin ana sa ran shugabannin zasu tattauna lokacin da NATO zata fice daga Afghanistan.

Sai dai Sakatare Janar na kungiyar kawancen Tsaro ta NATO, Anders Fogh Rasmussen, yace kungiyar ba zata yi gaggawar ficewa daga kasar Afghanistan ba, duk da bukatar kasar Faransa na janye dakarun ta.

Rasmussen yace, zasu ci gaba da zama a kasar har sai sun cim ma muradunsu na kare masu kai musu hari

“Muna cikin Afghanistan ne don kare ‘Yan ta’adda daga sake samun wurin zama, shirya kai muna hari a Turai da Amurka, saboda haka kare kasashen mu ya zama wajibi a duniyar mu ta yau” inji Rasmussen.

Wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Faransa, sakamakon zaben ya nuna kashi 84 na ‘yan kasar sun amince Faransa ta fice da dakarunta daga Afghanistan. Faransa dai tana dakaru 34,000 a Afghanistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.