Amurka

Shugaban Nukiliyar Amurka ya yi murabus

Gregory Jaczko shugaban hukumar Makamashin Nukiliyar Amurka
Gregory Jaczko shugaban hukumar Makamashin Nukiliyar Amurka REUTERS/Herwig Prammer

Shugaban hukumar makamashin Nukiliyan kasar Amurka ya bayar da sanarwar ajiye aikin shi, wata guda bayan da suka yi sa-in-sa da abokan aikin shi kan bukatar bayan da sha da a game da rashin hadarin shirin. Gregory Jackzo yace bayan da ya rike mukamin shi tsawon shekaru uku, lokaci ya yi da zai kare lafiyar jama’a ta wani bangaren, bayan ya ga abin da ya faru a Japan.

Talla

A watan Fabrairu Jaczko ya zamanto mutum na farko, da ya yi adawa da amincewa da kafa cibiyar nukiliyan farko na kasar  Amurka.

Yana mai nuna rashin amincewa ne kan batun rufa-rufar da ake kokarin yi bisa abinda ya auku a Fukushima, inda yake jaddada cewa a nasa tunani yin Murabus ne mafita.

Bayan da aka amince da kera sabbin Rumbunan sarrafa sarrafa Sinadarai kirar Toshiba masu karfin Megawart 1,100 a Georgia, Jackzo yace s ya bai wa sabon shugaban da za’a nada domin ya tanadi sabbin dabarun da zai fito dasu wajen amfani da makaman Nukiliya.

Fadar White House dai ta yabawa Jackzo, tare da bayyana anun nada sabon shugaban hukumar.

Wata Sanata a jam’iyyar Democrat Barbara Boxer ta yabawa Jackzo, akan yadda ya damu da kariyar lafiyar al’ummar Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.