Syria-MDD

Kofi Anan mai shia tsakani wajen warware rikicin kasar Syriya ya isa a birnin Damas

Kofi Annan
Kofi Annan Reuters

Manzon musamman na MDD da kungiyar Kasashen larabawa wajen warware rikicin siyasar kasar Syria, Kofi Annan ya isa a birnin Damas babban birnin kasar Syriya, domin ci gaba da tattauna samar da mafita a rikicin siyasar kasar.

Talla

Da yake magana dangane mutane 108 da aka kashe a karshen makon daya gabata, Kofi Annan yace babu shakka za a hukumta wadanda ke da hannu ciki wannan kazamin aiki.

A nasu bangaren yan adawa a kasar, sun nemi kasashen duniya su basu tallafin mai karfi, domin samun damar kare kansu daga muzgunawar da gwamnatin Bashar al Assad ke yi masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.