manyan kasashen duniya zasu kori jakadun kasar Syriya daga kasashensu
Wallafawa ranar:
Manyan kasashen duniya guda 7 da suka hada da Fransa, Amruka, Burtaniya, Spain Australiya, Jaus da kuma kasar Kanada sun bayyana korar jakadun kasar Syriya dake aiki a kasashensu, kwanaki bayan faruwar kisan rashin imanin kan fararen hular garin Hula dake tsakkiyar kasar Syriya, inda gwamnatin kasar ta yi amfani da makaman atilare a kansu.
Ministan harakokin wajen kasar Kanada John Baird ya kara da cewa, kasar kanada dai na sahun gaba daga cikin masu neman a maida shugaban kasar Syriya Bashar al Assad da gwamnatinsa saniyar ware a duniya, tare da ganin an magance matsalar ayukan jinkai da ke ci gaba da gurbacewa a kasar, M Baird ya baiwa jakadun tsawon kwanaki 5 da su tattara nasu ya nasu da iyalansu su fice daga kasar ta Kanada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu