Rasha-Amurka

Rasha ta gargadi Amruka cewa, kar sabon takunkuminta ya shafi kamfanoninta a kasar Iran

picture-alliance

 Kasar Rasha ta yiwa kasar Amruka barazana samun katafaren gibi ga huldar diflomasiyarsu, matsawar kamfanonin Rasha dake aiki a kasar Iran, sun cimma koma baya sakamakon sabon takunkumin da kasar Amruka ta kakabawa kasar.

Talla

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ministan harakokin wajen kasar ta Rasha ta fitar a yau talata ta bayyana cewa, muna tafiyar da kamfanoninmu ne, ba tare da sabawa takunkumin da MDD ta kakabawa kasar ba, dan haka muna son ganin basu faskanci wata takura ba daga sabuwar dokar kin jinin Iraniyawa da kasar Amruka ta saka.

Majiyar ta kara da cewa, idan kuma haka ta kasance, to’ zai haifar da babbar Baraka ga huldar diflomasiyar dake tsakanin Rasha da Amruka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.