MDD-Syria-China-Rasha

Kasahen China da Rasha sun ce basu yarda da kai wa kasar Syriya harin soja ba

Les corps de combattants tués, selon des opposants au régime,  par les forces de sécurité gouvernementales, sont alignés sur le sol d'une mosquée de Houla, près de Homs, le 26 mai 2012.
Les corps de combattants tués, selon des opposants au régime, par les forces de sécurité gouvernementales, sont alignés sur le sol d'une mosquée de Houla, près de Homs, le 26 mai 2012. Reuters / Houla News Network

Hukumar kula da kare hakkin bil’adam ta majailsar dunkin Duniya zata gudanar da taro na musamman kan kisan gillar da aka yiwa mutane a kasar Syria.  

Talla

Za’a dai gudanar da taron ne a birnin Houla, kuma kasashen Qatar, Turkiyya, Saudi Arebiya, Kuwait, Denmark da kuma Amurka duka sun bukaci taron ya tattauna kan abibda ya shafi keta ‘yancin bil’adama a kasar ta Syria.

A yayinda Kasar Sin wato China taki amincewa da shirin daukar matakin Soji ga kasar Syria, duk da rahotannin kisan mutane a kasar ta Syria.

Wannan matakin kin amincewar na China dai, ya biyo bayan da kasashe irin su Russia suka bayyana cewar lokaci ya yi daya kamata a dauki mataki akan kasar ta Syria.

Shugaban kasar Faransa Francious Hollande, tare da shugabannin manyan kasashen Duniya duk sunki amsa bukatar janye dakaru a kasar ta Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.