Faransa-Colombia

‘Yan tawayen FARC a Colombia sun saki Dan Jaridar Faransa

Romeo Langlois dan Jaridar Faransa da 'Yan tawayen Colombia suka yi garkuwa da shi
Romeo Langlois dan Jaridar Faransa da 'Yan tawayen Colombia suka yi garkuwa da shi AFP PHOTO/Luis Acosta

‘Yan Tawayen kungiyar FARC ta kasar Colombia sun saki Romeo Langlois, Dan Jaridar kasar Faransa da suka yi garkuwa da shi wata guda da ya gabata, ‘Yan tawayen sun mika Dan Jaridan ne ga kungiyar agaji ta Red Coss, inda ya shaidawa manema labarai c yana cikin koshin lafiya.

Talla

‘Yan Tawayen sun raka Dan Jaridar har kauyen da aka mika shi, kafin suka koma cikin daji.

A ranar 28 ga watan Afrilu ne ‘Yan tawayen a Colombia suka yi garkuwa da dan Jaridar a yankin Caqueta a wani batakashi da suka yi da dakarun Colombia.

‘Yan tawayen FARC sun dade suna yaki a yankin Latin Amurka tun a shekarar 1964. Kungiyar ta samo asali ne daga kungiyar masu fataucin miyagun kwayu wadanda suka kaddamar da yaki da gwamnatin Colombia shekaru 50 da suka gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.