Syria

Taron kan kasar Syria a Paris

Reuters

Yayin da yua juma’a ake fara taro na musamman don duba mafita kan rikicin kasar Syria, Amurka na shirin wuce wa gaba don kiran mahalarta taron na birnin Paris su kakaba wa kukumomin birnin Damascus Karin takunkumi masu tsauri.Wani jami’in kasar da ke Magana jim kadan bayan da sakatariyar harkokin wajen amurka Hillary Clinton ta kama haryar zuwa Fransa, yace lokaci ya yi da za a hada hannu don goya wa kwamitin tsaron MDD ya kara matsin lamba ga gwamnatin shugaba Bashar al Assad.Ya ce da dama daga cikin kasashen da ke halartar taron sun riga sun sanya wa Syria takunkumi,amma akwai bukatar daukar matsayi na bai daya.