Iran-Syria

Iran ta jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Assad na Syria

Shugaban kasar Syria Bashar el-Assad a lokacin da ya ke ganawa da jekadan Iran Saïd Jalili à birnin Damascus
Shugaban kasar Syria Bashar el-Assad a lokacin da ya ke ganawa da jekadan Iran Saïd Jalili à birnin Damascus REUTERS/SANA/Handout

Kasar Iran ta sake bada goyan bayanta ga gwamnatin shugaba Bashar al Assad a wata ganawa da aka nuna shugaban da wani babban jami’in kasar, yayin da dakarun Syria ke ci gaba da musayar wuta tsakanin su da ‘Yan Tawaye a yankin Arewacin Aleppo.

Talla

Shugaban Majalisar Tsaron Iran, Saeed Jalili, yace ba zasu bari kasashen duniya su gurgunta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ba, sakamakon tashin hankalin da ake samu a kasar.

Iran kuma ta zargi Turkiya da hura wutar rikicin Syria.

Kasar Iran kuma, ta zargi kasar Turkiyya da Qatar wajen bai wa ‘Yan tawaye makaman yaki da gwamnatin shugaba Bashar Assad. Zargin da kasar Turkiyya ta karyata a tashin hankalin da aka kwashe watanni 17 ana fama da shi a kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI