Isra'ila-Iran

Isra’ila ta inganta na’ura mai iya kakkabo makaman kare dangi

Firaministan Isra'ila Benjamin Natenyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Natenyahu Reuters/Lior Mizrahi/Pool

Kasar Isra’ila, ta kara inganta na’urar maganadisunta mai iya kakkabo makaman kare dangi, a wani matakin shirin ko-ta-kwana da ta ke dauka kan kasashen Iran da Syria.Kasar Isra’ila tana ganin na’urar zai ba ta damar magance duk wata barazanar da za ta iya fuskanta daga kasashe kamar Iran da Syria.

Talla

Kirkiro da wannan na’urar mai sifar Akwati, kamar yadda kasar Isra’ila ke cewa, zai taimaka ga inganta na’urorin da yanzu haka kasar ta ke da su.

Isra’ilan tace yanzu ana cikin wani zamani ne, na wanzuwar fasahar kere-kere, da kuma ake amfani wajen samun kariya daga tanade-tanaden abokan hamayya.

Babban jami’in tsaron kasar Isra’ila yace na’urar ta maganadisu, tana da karfin iya sunsuno duk wani harin da abokan gabarsu ke iya kai masu.

An dai fito da wannan sabuwar fasahar ta na’urar kakkabo makamai ta kasar ne a shekarar 1990, domin maganin harin da kasar ke iya fuskanta daga kasashe kamar Syria da Saudi Arebiya, da kuma Iraqi.

A watan jiya ne kasar Iran ta gwada makaminta mai linzami da ke iya cin nisan kilomita 2000, abinda ya tayar da hankalin Isra’ila da ke makwabtaka da kasar wanda nisan da ke tsakanin kasashen bai wuce kilomita 1000 ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.