Rasha

Kotun Rasha ta samu mawakan Band Pussy Riot da laifi

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin

Wata kotu a birnin Moscow ta sami uku daga cikin mawakan kungiyar band Pussy Riot da laifin shirya boren kin jinin gwamnatin Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha a wata Coci.

Talla

Mai Shari’a, Marina Syrova, a yayin da ta ke gudanar da shari'ar, ta ce mawakan sun shirya boren ne na watan Febrairun da ya gabata a cikin Cocin Saviour Cathedral kuma a tsanake.

Ana kuma sa ran za ta yanke musu hukunci a inda mai shigar da kara ke neman a yanke musu hukunci daurin shekaru uku a gidan a yari matsayin hanyar gyara halayensu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.