Faransa ta goyi bayan haramta shawagin jirage a Syria
Wallafawa ranar:
Gwamnatin kasar Faransa tace za ta bayar da goyon bayan haramta shawagin jiragen sama a kasar Syria domin sassauta luguden wuta daga bangaren dakarun Gwamnatin Bashar al Assad a birnin Damascus da yankin Aleppo.
Sai dai Ministan harakokin tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, ya yi gargadin haramtawa jiragen Gwamnatin Syria shawagi na iya jefa kasar cikin yaki inda kuma har yanzu kasashen Duniya bas u cim ma matsaya ba game da shiga tsakanin rikicin kasar.
Amma kuma Mista Le Drian yace Faransa ba za ta Amince da Sauyi ba a Syria har sai Bashar Assad ya yi murabus.
Tun a farkon watan Agusta Sakatariyar Harakokin Faransa Hillary Clinton ta nemi tattauna batun haramta shawagin jirage, tana mai cewa Turkiya da Amurka sun amince su tattauna game da batun amma kasar Rasha ta yi wasi da kudirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu