Italiya

Wani babban ‘Yan Katolikan kasar Italiya ya rasu

Marigayi, Carlo Maria Martini
Marigayi, Carlo Maria Martini Wikipedia

Wani babban shugaban addinin Kirista na mabiyan Katolika da ke kasar Italiya, Carlo Maria Martini, ya rasu.

Talla

Martini, wanda ya taba kawo muhawarar a canza tunani akan al’amuran zamani, ana ganin ya na daya daga cikin wadanda za su gaji babban shugaban ‘Yan Katolikan duniya, wato Paparoma.

Ya yi fama ne da ciwon makeketa na tsawon shekaru da dama inda lafiyarsa ta kara tabarbarewa a ‘yan makwannin nan.

Ya rasu ne a Birnin Milan, inda ya dade ya na zama shekaru da dama da su ka wuce.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.