Angola

Dos Santos ya lashe zaben Angola

Shugaban kasar Angola, Jose Eduardo Dos Santos, da jamiyyar sa MPLA sun sake samun nasaran zarcewa da mulkin kasar, a babban zaben kasar da akayi ranar Asabar, da ta gabata, wanda kuma ya sha suka daga ciki da wajen kasar.Zaben wanda akayi ranar Juma’a na nuna cewa shugaban ya sami kuri’u kashi 74% na yawan kuri’un da aka jefa.  

Shugaban kasar Angola, Dos Santos
Shugaban kasar Angola, Dos Santos REUTERS/Siphiwe
Talla

Karkashin sabon kundin zaben kasar ta 2010, Shugaban, wanda cikin wannan makon zai cika shekaru 70, ya sake samun sabon wa’adi na shekaru 5.

Ya dai riga ya kwashe shekaru 33 yana mulkin kasar.

Da yammacin jiya kuma masu sa idanu daga kasashen waje karkashin, Pedro Verona Pires, dake jagorantar wakilan Kungiyar kasashen Africa sun ce babu magudi a sake zaben Santos da akayi.

Tuni dai kafofin yada labaran kasar musamman mallakar kasar su ka daukan a shafukan farkon na nasarar da Santos ya samu.

“Babban nasara ga jam’iyar MPLA”, inji jaridar Jornal de Angola, wacce mallakar gwamnatin kasar ce.

Rashin murnar dab a yi a babban birnin kasar ba, inji masa sa ido akan siyasar duniya ya nuna cewa, da yawa daga cikin ‘Yan kasar, basu yi mamaki da sakamkon zaben ba.

Santos, ya kasance shugaban kasa na a nahiyar Afrika da ya dade a kan karagar mulki bayan shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI