Syria

Jirgin yaki ya kashe mutane 18 a Syria

Wani jirgin yakin dakarun Syria da yayi lugudan wuta a yankin Al –Bab da ke garin Aleppo ya kashe mutane 18, cikinsu maza goma, mata shida da kuma yara biyu.

Wani hari da aka kai yankin Salah al-Din a garin Aleppo
Wani hari da aka kai yankin Salah al-Din a garin Aleppo Reuters/路透社
Talla

A cewar wata kungiyar mai saka ido akan riki na Syria, dakarun gwamnati wadanda ake zargi da kai harin sun sun yi wani lugudan wusu Gundumomi a garin na Aleppo kamar yadda, shugaban kungiyar kare hakkin Dan Adam, Syrian Observatory for Human Rights, Abdel Rahman ya fadawa Kamfanin Dillancin labaran AFP.

Kamfanin Dillancin labaran kasar, na SANA, a ranar Litinin ya bayyana cewa, dakarun kasar na ta kokarin korar ‘Yan tawayen kasar, wadanda a cewar SANA sun samu rashin nasara da dama.

Akalla dai mutane sama da 26,000 ne su ka rasa rayukansu a rikicin na Syria wanda ya fara tun a watan Maris din bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI