MDD-FAO

Frashin abinci ya gagara daidaituwa, in ji Majalisar dinkin duniya

Hukumar kula da abin Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya tace akwai yiyuwar za’a iya shiga halin tsadar kayan abince akamr yadda aka taba samu a shekarun baya, al’amarin da ya haddasa bore a sassan kasashen Duniya. Hukumar tace, ya zuwa makon nan kasashen duniya suna iya kokarin kare aukuwar matsalar hauhawan kayan abincin, tare da kira ga kasashe su haramta fitar da kayyakin abinci zuwa wasu kasashe.Hukumar tace babu wani sauyi da aka samu na saukar farashin hatsi da gyada da waken Soya, da nama da kuma farashin Suga.Sai dai hukumar ba tace, ko wannan zai shafi kasashen Afrika ba, amma kuma wani rahoton majalisar Dinkin duniya ya nuna kasashen yankin sahel na fuskantar karancin Abinci, saboda tashin hankalli da kuma ambaliyar Ruwa. 

Graziano da Silva, Shugaban hukumar Noma da Abinci ta majalisar dinkin duniya   (FAO).
Graziano da Silva, Shugaban hukumar Noma da Abinci ta majalisar dinkin duniya (FAO). REUTERS/FAO HO/Giulio Napolitano