Girgizan kasa ta kashe mutane 43 a Sin
Akalla mutane 43 sun rasa rayukansu a wasu jerin girgizan kasa da su ka auku a kudancin kasar Sin. Kamfanin Dillancin labaran AFP ya rawaito cewa,wasu mutane sama da 150 kuma sun jikkata, a yayin da wasu sama da 100,000 su ka rasa matsugunansu sanadiyar girgizan kasar wacce ta auku a yankunan Yunnan da Guizhou.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da hukumar hulda da jama’a ta kasar ta fitar ta ynar gizo ta tabbatar da mutuwar mutane 43, sannan kuma gidaje 20,000 sun rushe.
A cewar hukumar da ke binciken doron kasa ta kasar Amurka, girgizar farko ta auku ne da misalin 11.20 na safe sannan sai ta biyu kuma bayan sa’a daya.
Dukkanin girgizan inji hukumar na da karfin maki 5.6.
Kudancin kasar Sin na awan fama da girgizan kasa inda a watan Mayun da ya gabata ne girgizan kasa mai karfin maki 8.0 ta auku a yankin Sichuan da wasu yankunan Shaanxi da kuma Gansu, inda su ka kashe dubbannin mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu