Faransa

Hollande ya dauki alwashin kama wadanda su ka yi kisan Alps

Shugaban kasara Faransa, François Hollande
Shugaban kasara Faransa, François Hollande Reuters

Shugaban kasar ta faransa Francois Hollande, ya sha alwashin daukar matakin farautar wadanda suka bindige wasu Turawan Birtaniya cikin motarsu a lokacin da suke shakatawa a yankin Alps. Wannan kuma na zuwa ne bayan Firaministan kasar Jean Marc, ya ce zasu dauki matakin magance matsalar tsaro a yankin Marseille da ke fama da gungun ‘Yan bindiga dadi. 

Talla

A yanzu haka dai ‘Yan sanda na kokarin samar da amsa ga kisan na mutanen.
 

Mai shigar da kara,  Eric Maillaud, ya bayyana wannan kisa a matsayin wani aikin na rashin tausayi.

Sai dai ya kara da cewa, har yanzu basu gaza domin sai sun zakulo wadanda su ka yi kisan.
“Binciken da za gudanar akan gawawwakin zai kara mana bayanai game da kisan,” inji Maillaud.

An dai tsinci gawawwakin wadanda aka kashe ne da wasu yara mata da su ka tsira a ranar Laraba a wani daji kusa da kauyen Chevaline da ke yankin Haute-Savoie a kasar Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI