Amurka-Afghanistan

Amurka ta mika ragamar jagorancin gidan yarin Bagram ga Afghanistan

Dakarun Amurka sun mika ragamar ikon gidan yarin Bagram da ake tsare da hursunoni 3,000 da suka kunshi mayakan Taliban ga gwamnatin Afghanistan, amma Amurka tace har yanzu ita ke da ‘yancin kamawa da tasa keyar mutane zuwa gidan yarin.Wannan yunkurin shi ne mataki na karshe na mika daukacin gidajen yarin ga hukumomin kasar Afghanistan, kafin ficewar dakarn NATO a shekarar 2014.

'Yan gidan yarin Bagram a kasar Afghanistan
'Yan gidan yarin Bagram a kasar Afghanistan DR
Talla

Shugaba Hameed Karzai yace shirin mika gidan yarin, wata nasara ce ga samun Yancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI