Iran-Masar-Syria

Za’a tattauna rikicin Syria tare da Iran a Masar

Kasar Iran tace zata halarci wani taron kasashe hudu a Masar, wadanda za su yi nazarin samo hanyoyin magance tashin hankalin da a ke ci gaba da samu a kasar Syria. Kasashen da za su halarci taron sun hada da Turkiya da Masar da Saudi Arebiya.

Wano hoton Shugaban Syria Bashar Assad a cikin shara
Wano hoton Shugaban Syria Bashar Assad a cikin shara REUTERS/Shaam News Network
Talla

Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian ne ya tabbatar da halartar Iran zuwa taron, akan hanyarsa ta zuwa birnin Alkahira.

Wannan ya zama wani yunkuri na farko da kasashen duniya suka sanya Iran, mai karfin fada aji a Syria, don shiga a dama da ita, wajen sasanta rikicin kasar.

Kasar Masar ce ta dauki wannan matsayi na sanya Iran cikin lalubo hanyar kawo karshen rikicin na Syria, kuma ana sa ran Iran za ta yi amfani da matsayin ta wajen tirsasaswa shugaba Bashar al Assad.

Amma kuma a daya bangaren, shugaban kwamitin tsaro da harkokin diflomaiysa na Majalisar kasar Iran, Aladin Borujerdi, ya bukaci hadin kan kasashen da ke halartar taron, dan samun daidaito, ganin yadda wadanda ke adawa da shugaba Assad suka fi yawa a zaman taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI