Zawahiri ya tabbatar da mutuwar mataimakinsa al Libi,
Wallafawa ranar:
Shugaban Kungiyar Al Qaeda, Ayman Zawahiri, ya tabbatar da mutuwar maitaimakinsa Abu Yahya al Libi, sakamakon wani harin sama da aka kai Yankin Waziristan na kasar Pakistan a ranar Hudu ga watan Yunin bana. Sakon Bidiyon kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka ke tuna harin 11 ga watan Satumba.
Sakon Bidiyo na tsawon minti 42, Zawahiri ya bayyana shugaban Amurka, Barack Obama a matsayin makaryaci, wanda aka zaba don yaudarar Musulmin duniya, da kuma ake samun nasara akansa a kasar Afghanistan.
Zawahiri ya kuma tabbatar da cewa suna rike da wani ma’aikacin agaji Dan Amurka, Warren Weinstein, har sai Amurka ta saki mabiyansu.
Jami’an Amurka sun ce a ranar Litinin ne aka saka bidiyon a Intanet mai taken ‘Zakin ilimi da Jahadi”. Wanda ya nuna Zawahiri karon farko cikin watanni uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu