Syria

Brahimi ya kama hanyarsa ta zuwa Damascus

Wakili kasashen larabawa da Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan rikicin Syria, Lakhdar Brahimi
Wakili kasashen larabawa da Majalisar Dinkin Duniya na musamman akan rikicin Syria, Lakhdar Brahimi REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/Files

Sabon wakili na musamman da kasashe larabawa da Majalisar Dinkin Duniya su ka nada, Lakhdar Brahimi ya kama hanyar ta zuwa Damacus da ke kasar Syria. Brahimi shi ne ya canji, tsohon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, bayan ya  ajiye aikin na nashi a watan Agustan da ya gabata. 

Talla

Anan a lokacin ya fadi cewa baya samun goyon baya a aikin nasa wanda hakan ya sa ajiye aikin.

Shi dai Brahimi, ana sa ran zai zamanto wikili ne mai shiga tsakanin gwamnatin Shugaba Bashar –al Assad da ‘Yan tawayen kasar a rikicin na Syria da ya ki ci ya ki cinyewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.