Jami’an tsaron Mexico sun cafke wani shugaban masu safarar miyagun kwayoyi
Jami’an Tsaro a kasar Mexico, sun yi nasarar kama shugaban masu safarar miyagun kwayoyi, Jorge Eduardo Costilla Sanchez, wanda duniya ke nema ruwa a jallo. Rundunar sojin ruwan kasar, ta ce an kama Costilla ne a Jihar Tamaulipas, da ke Arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Costilla Sanchez, ya kasance yana daga cikin jerin sunaye guda 37 a cikin masu safaran miyagun kwayoyi, inda har aka saka tikwicin kudi na Dalar Amurka miliyan 2.2 ga duk wanda ya kama shi.
Kama Costilla Sanchez, ya zo bayan mako daya da cafke wani babban masu sarafan kwayoyin, Mario Cardenas Guillen, a Tamaulipas, wanda aka fi yiwa lakabi da “El Gordo”, wato “Dan luti.”
Kungiyar masu safarar miyagun kwayoyin a kasar Mexico dai ta fashe zuwa gida biyu, bayan Dan uwan Cardenas, Antonio Cardenas, ya mutu a wani musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu safarar kwayoyin a shekarar 2010.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu