Amurka-Saudiya

‘Yanci zai hana Amurka daukar matakin hukunta wadanda suka ci mutuncin Musulunci

Gwamnatin Saudiya da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah Waddai da Wani Shirin Fim na wani Ba’amurke da ke nuna cin Zarafin Addinin Musulunci wanda ya janyo barkewar Zanga Zanga a kasashen Musulmi. Amma gwamnatin Saudiya tace kai wa ofishin jekadancin Amurka hari kuskere ne.

sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Hillary Clinton
sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Hillary Clinton REUTERS/Gary Cameron
Talla

Bayan barkewar Zanga zangar a kasashen musulmi, ‘Yanci zai hana Gwamnatin Amurka daukar matakin hukunta wadanda suka samar da Fim din karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Fim din wanda ya sabawa Al’ummar Musulmi saboda cin Zarafin Manzon Allah ya yadu a kasashen Duniya musamman kasashen Gabas ta Tsakiya da kasashen Arewacin Afrika.

Wani Fasto ne mai suna Nakoula Basseley Nakoula, mazauni Califonia shi ne ake zargin ya Samar da Fim din. Kuma ya yada Fim din zuwa ga mabiyansa da Shafin intanet na Fasto Terry Jones wanda a kwanan nan baya ya Kona al Kur’ani Mai girma.

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton tace Mutane ba za su fahimci dalilin da ya sa Amurka ba za ta iya kare aukuwar irin wannan al’amari ba.

“Muna da al’adar ‘Yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya ba mu a kasarmu, kuma ba za mu iya hana ‘Yan kasa fadin albarkacin bakinsu ba koda abin da za su fada sabo ne” a cewar Hillary Clinton.

Yanzu haka bangaren Shari’ar Amurka ya kasa fito da hanyar hukunta Nakoula da mabiyansa. Kuma masana sun ce babu wani abu da bangaren shari’ar zai yi domin haramtawa Amurkawa ‘Yancin da kundin tsarin mulki ya ba su.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi Allah waddai da Fim din wanda ya Haifar da Zanga-zanga a kasashen Musulmi.

Bayan fito da Fim din ne Al’ummar Musulmi a Libya da Masar da Yemen da wasu kasashen Musulmi suka kaddamar da hare hare a Ofishin jekadancin Amurka wanda ya yi sanadiyar kisan wani babban Jami’in Jekadancin Amurka a Benghazi.

Sai dai Gwamnatin Saudiya duk da ta yi Allah waddai da fito da Fim din wanda ya ci zarafin Musulmi amma kuma tace kaddamar da hare hare a Ofishin jekdancin Amurka kuskure ne.

Yanzu haka an rufe Filin saukar jirgin birnin Benghazi inda aka kashe Jekadan Amurka.

A kasar Yemen kuma an samu mutuwar mutane Hudu sanadiyar Zanga-zangar la’antar Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI