Colombia ta cafke babban mai safarar miyagun kwayoyi a kasar
Hukumomi a Kasar Colombia, sun sanar da kama daya daga cikin fitattun masu safarar miyagun kwayoyi a kasar, Daniel Barrera, wanda aka fi sani da Crazy Barrera. Shugaban kasar Colombia, Juan Manuel Santos, wanda ya ce an kama shi ne a Venezuela, ya bayyana Barrera a matsayin mutumin da aka fi nema a wanna lokaci.
Wallafawa ranar:
A cewar Santos, hukumar leken asirin kasar Amurka, ta CIA da kuma hukumar leken asirin kasar Birtaniya ta M16 sun taimaka wajen cafke Barrera.
Barrera, wanda ake zargin ya yi safarar miyagun kwayoyi sama da tan 900 zuwa cikin kasar Amurka da kuma kasashen nahiyar turai, an kama shi a garin San Cristobal da ke kasar Vebezuela.
Ana kuma zargin yana da alaka da ‘Yan kungiyar ‘Yan tawayen kasar ta Colombia.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Venezuela, Tareck Al Aissami, wanda ya tabbatar da kama Barrera a shafin Twitter, ya bayyan cewa, wannan kamu babban kamu ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu