Rasha

Rasha ta umurci hukumar USAID da ta fice daga kasarta

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin 路透社

Gwamnatin Kasar Rasha ta dakatar da aiyukan hukumar cigaba ta kasar Amurka, wato USAID, bayan ta kwashe sama da shekaru 20 tana aiki a cikin kasar. A wani yanayi dake nuna tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu, Rashan ta bukaci hukumar cigaba ta Amurka da ta dakatar da aiyukan ta a cikin kasar. 

Talla

Shugaban kasa, Vladimir Putin, ya zargi hukumar da tinzira ‘Yan kasar suna gudanar da bore da kuma adawa da Gwamnati, musamman kungiyoyin fararen hula.

Ita dai wannan hukuma, ta ce ta kashe kusan Dala biliyan uku, wajen yaki da cutar kanjamau da tarin Fuka a kasar, tare da taimakawa nakasassu, kare muhalli da kuma yaki da fataucin mutane.

Yayin da take mayar da martani kan dakatarwar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, ta ce duk da korar hukumar daga cikin Russia, za su cigaba da taimakawa wajen gina demokradiya, kare hakkin Bil Adama da kuma taimakon kungiyoyin fararen hula.

Ita dai wannan hukuma ta USAID tana gudanar da aiyukan ta a kasashe sama da 100, wajen yada manufofin harkokin waje na kasar Amurka.

Kungiyoyin fararen hula da dama sun bayyana bacin ransu da matakin.

An dai ba hukumar ta USAID, wa'adin kasa da makwanni biyu da ta fice daga kasar ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.