Japan

Ban ya nemi Japan da Sin su sasanta tsakaninsu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-mooon
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-mooon

Sakateren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a Japan da China, inda ya bukaci kasashen biyu da su kai zuciya nesa, wajen magance rikicin dake tsakanin su.

Talla

Ban ya nemi shugabanin biyu, da suyi amfani da taron Majalisar Dinkin Duniya makon gobe, wajen rage tankiyar.

“A matsayi na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, babu daman a dauki matsayi akan wannan takaddama.” Inji Ban

Rikicin dai ya samo asili ne akan wasu tsibirai da ke gabashin kasar Sin wanda aka fi sani da Senkaku a Japan kana ana kiransu Diaoyu a kasar Sin.

Kasar Japan ce dai ke kula da tsibiran a yanzu, amma kasar Sin da Taiwan na ikrarin tsibiran na su ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.