Faransa

Faransa ta tsaurara matakan tsaro a ofisoshin Jakadancinta dake kasashe 20

Gwamnatin Faransa ta ce ta kara daukan matakan tsaro a ofisoshin Jakadancin ta dake kasashe 20, saboda tsoron abinda zai biyo baya, sakamakon wallafa wasu hotuna da wata mujallar kasar tayi, wanda ta danganta su da Manzan Allah wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Ministan harkokin wajen kasar, Laurent Fabius ya ce daukar matakin ya zama wajibi, saboda yadda Mujallar ta batawa al’ummar Musulmi rai.

“Na bada umurnin kara matakan tsaro a ofishoshin Jakadancin mu dake kasashen duniya, na kuma bukaci Yan kasar Faransa suyi taka tsan tsan duk inda suke.” Inji Fabius.

A wani bangare kuma, Editan Mujallar ta Charlie Hebdo da ta wallafa zanen, ya kare matakin da suka dauka na wallafa zanen da suka danganta da Manazan Allah wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi, abinda ya harzuka Musulmin duniya.

“Aikin mu shine wallafa labaran duniya, muna mamaki ko yaushe mukayi labarin day a shafi addini, sai ace mana muna tada hankali, ba tada hankali bane, mu mujalla ne masu sharhi da shagube kan abubuwan da suke faruwa, mun yi aikin mu ne kawai, ba wai tada hankali.” Inji Editan Mujallar Gerard Biard a hirarsa da gidan Radiyo Faransa.

A jiya ma kasar ta Faransa ta bada umurnin rufe makarntunta da ke kasar Masar da Tunisia domin tsoron kada a kai masu hari.

An fitar da sanarwar kulle makarantun ne daga jiya laraba zuwa Litinin a kasar Tunisia, a yayin da a kasar Masar za a kulle daga ranar Alhamis.

Jam’iayar Islamist Ennahda wacce ke mulki a kasar Tunisia ta yi kira da ayi zanga zangar lumuna akan zanen wanda ta misalta shi a matsayin “sabon hari akan Annabi Muhammad” wanda tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI