Amurka

Amurka ta dage takunkumi kan kasar New Zealand

Sakataren tsaron kasar Amurka, Leon Edward Panetta
Sakataren tsaron kasar Amurka, Leon Edward Panetta REUTERS/Yuri Gripas

Kasar Amurka ta dage takunkumin da ta kakabawa jiragen ruwan kasar New Zealand na kada su shiga filayen jiragenta na ruwan kasar tun a shekarun 1980. Wannan dai ana ganin wata hanya ce da kasashen biyu ke so su kyautata dangantakar da ke tsakaninsu tun bayan tabarbarewar lamurra a tsakanin kasashen biyu a lokacin yakin cacar baki. 

Talla

Haka kuma wannan matakai da Amurka ta dauka zai samu amincewar shugaban tsaro na kasar ta Amurka.

Ziyarar da Panetta yak ai zuwa kasar New Zealand, ita ce ziyara ta farko wacce shugaban Pentagon zai kai a cikin shekaru 30 da su ka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.