Habasha

An rantsar da Hailemariam a matsayin sabon Firaministan Habasha

An rantsar da sabon Firaministan kasar Habasha, Hailemariam Desalgn a yau Juma’a, bayan mutuwar tsohon Firaministan kasar, Meles Zenawi. “Ni, Hailemariam Desalegn, a gaban ‘Yan majalisun kasa, na yadda da zama Firaministan kasar Habasha,” Hailemariam, ya ce a dai dai lokacin da ‘Yan majalisun ke buga teburansu domin nuna amincewarsu.  

Sabon Firaministan kasar Habasha
Sabon Firaministan kasar Habasha cdn.thehabariannetwork.com
Talla

Dan shekaru 47, an zabi Hailemariam, a satin da ya gabata ne a matsayin shugaban jam’iya mai mulki ta EPRDF,wacce ke da mafi rinjaye a majalisar kasar.

“Da wannan shawara ta jam’iyar PRDF da ‘Yan majalisu, ina mai matukar farin cikin karban wannan mukami na Firaministan”, Hailemariam ya kara fada, bayan ya yi rantsuwa da Bible a hanunsa.

Ya kuma daukin alwashin cewa, zai cigaba ayyukan da marigayi Zenawi ya shata, inda ya kara da cewa, “Mun kawo zaman lafiya da Demokradiya da kuma cigaba a kasarmu”

“Meles ya dauki kansa a matsayin bawan mutanen kasar nan, saboda haka bazan canja wani abu daga irin ayyukan day a shata ba.”

Hailemariam ya fito daga cikin ‘Yan kabilar Wolayta daga kasashen Kudancin kasar, inda ya yi mulki a matsayin shugaba na shekaru biyar.

Meles dai ya rasu ne yana dan shekaru 57 bayan ya sha fama da jinya, wanda kuma ake mai kallon gwarzon Afrika saboda rawar da ya taka a yankin na wanda na ‘Yan Al Qaeda ne, sai dai ana kuma sukansa akan tauye hakkin Bil Adama.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI