Birtaniya, Faransa da Jamus na neman a kara kakabawa Iran sabbin takunkumi
Kasashen Britaniya, Faransa da Jamus, sun yi kiran karawa kasar Iran sabbin takunkumi, a karkashin kungiyar kasashen Turai, saboda shirin kasar na samun makamin Nukiliya. Ministocin harkokin wajen kasashen uku, suka gabatar da wanna bukata, a wasikar da suka rubutawa Babbar Jami’ar Diplomasiyar kungiyar, Catherine Ashton, saboda fito na fiton da ake tsakanin bangarorin biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad, ya kuma gana da Babban Sakataren, Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki- moon a ranar Lahadi, a dai dai lokacin da shugaban tsare-tsaren harkokin wajen Nahiyar Turai, ya tattauna akan kasar ta Iran tare da Sakatariyar Harkokin wajn kasar Amurka, Hillary Clinton.
Kasar Amurka da mukarrabanta na zargin kasar Iran da kokarin kera makamin Nukiliya, amma kasar ta Iran ta musanta hakan inda t ace za ta yi amfani dashi wajen samar da wuta.
Har ila yau kasashen, Amurka, Birtaniya da Faransa, sun yi gargadi a gaban Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya, cewa lokaci na kurewa na ganin cewa a sasanta takaddamar.
Ban dai ya yi kira ga Iran da ta yi kokari ta bawa duniya hujjra cewa ba makamashi Nukiliya ta ke kokarin kerawa ba.
Wanna takaddama ta Iran, na daya daga cikin manyan batutuwab da za su ja hankalin mutane a taron na Majalisar Dinkin Duniya, wanda za a fara shi a gobe a birnin New York.
Tuni dai kasar Isra'ila, na barazanar kai hare-hare kan kasar ta Iran akan batun, sai dai kasar Amurka na nuna mata cewa batun bai kai ga haka ba a yanzu.
Haka kuma, Ahmadinejad, zai gabatar da jawabinsa a gaban kasashen duniya a ranar Laraba, inda kuma halartarsa wannan taron ita ce zata zamanto na karshe a matsayinsa na shugaban kasar Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu