Kotu ta yankewa tsohon shugaban 'Yan sandan kasar Sin, shekaru 15
Wata Kotu a kasar China, wato Sin, ta daure Tsohon shugaban ‘Yan Sandan kasar, Wang Lijun, shekaru 15 a gidan yari, saboda samun sa da laifin cin hanci, kokarin gudu ya bar kasar, da kuma rufawa matar Bo Xilai asiri, sakamakon kashe wani Dan kasuwa da tayi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotun tace ta saukaka masa hukuncin ne saboda yadda ya taimaka mata daga bisani, wajen bada shaidar da aka daure matar Dan siaysar, Gu Kilai.
Har ila yau, Kotun tace an daure Wang shekaru tara saboda cin hanci, shekaru bakwai na karya doka, kana shekaru bibbiyu na amfani da mukamin sa wajen aikata laifufuka da kuma kokarin gudu, amma an rage masa zuwa shekaru 15 gaba daya.
Dangantaka tsakanin Bo da Wang ta yi tsamari ne a farkon shekarar nan, watanni bayan an sami wani abokin iyalan Bo a mace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu