Masar

Morsi ya ki amincewa da kai sojojin kasashen waje Syria

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi
Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi REUTER/Handout

Shugaban Kasar Masar, Mohammed morsi, yace ko da sunan wasa baya goyan bayan shirin kai sojojin kasahsen waje Syria, dan magnce rikicin da kasar ke fama da shi, sai dai ya bayyana goyan bayan sa na ganin shugaba Bashar al Assad ya sauka daga karagar mulki.

Talla

Yayin da yake bayani a New York, shugaba Morsi yace kasashen Masar, Iran, Saudi Arabia da Turkiya na kokarin diplomasiya na kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe watanni 18 anayi a kasar, wanda ake zaton yanzu haka ya lakume rayukan mutane kusan 29,000.

“Ni ban amince da kai sojojin kasashen waje kasar Syria ba, ina ga kuskure ne babba idan aka yi haka: inji Morsi.

Ya kara da cewa ya gayyaci shugabanni daga kasarsa, da Saudiya, da Iran da Turkia domin a samo hanyar magance matsalar ta Syria.

A Gobe ne ake sa ran Morsi zai bada jawabinsa a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI