Syria

Ban Ki-moon ya ce rikicin Syria na iya hargitsa Yankin Gabas ta Tsakiya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin duniya, Ban Ki - moon, ya janyo hankalin shugabanin kasashen duniya, cewar rikicin Syria na cigaba da tabarbarewar da kan iya shaifar Yankin Gabas ta Tsakiya baki daya. Yayin da yake bude taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 67, Ban yace ya zama wajibi duniya ta hada kai domin kawo karshen wannan al’amari, inda ya kara da cewa rikicin na kara tabarbarewa.  

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon fr.rian.ru
Talla

“Rikicin Syria na dada tabarbarewa kowacce rana, tashin hankalin ba wai ya tsaya a Syria bane kawai, ya shafi Yankin da kuma duniya baki daya, wannan barazana ce ga zaman lafiyar duniya, wanda ke bukatar daukar mataki a kwamitin Sulhu.”

Ya kara da cewa “ina kira ga kasahsen duniya da kwamitin Sulhu da su baiwa Lakhdar Brahimi goyan baya, dan kawo karshen halin da ake ciki.”

Ana shi bangaren, Sarkin kasar Qatar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Al Thani, wanda ke goyon bayan Bashar al- Assad, ya ce mafita ita ce a hada dakarun kasashen labarawa su shiga tsakanin rikicin.

“Gara kasashen larabawa su isu su shiga tsakani, domin ganin an kawo karshen asarar rayuka da ake yi. A kasar.” Inji Khalifa.

Haka kuma, Shugaban kasar Amurka,Barack Obama, ya yi jawabi akan kasar Iran wacce ake zargi da kera makamin Nukiliya, da kuma batun barazanar da kasar Isra’ila ke yi na kaiwa Iran hari.

“Babu shakka, barin kasar Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba abu ne da za a kau da kai ba, domin zai yi barazana ga kasar Isra’ila, tsaron yankin kasashen Yankin Gulf da kuma tattalin arzikin duniya.” Inji Obama.

Haka shima Ban, ya nuna damuwarsa akan takaddamar ta Iran, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su gujewa yin amfani da karfin Soja wajen ganin an magance matsalar, wacce ya ce kan iya zama bala’i.

Shugaban Iran, Mahmud Ahmadinejad, wanda shi ma ke halartar taron a birnin New York, ya yi watsi da maganganun da ake yi, inda ya kara da cewa, babu yadda za’a yi su bar shirin wanda kasar ke yi don samar da makamashin wuta ba na Nukiliya ba.

A yau ne Ahmadinejad zai gabatar da jawabainsa a gaban Mjalisar Dinkin Duniyan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI