Iran

Ahmadinejad ya zargi Isra’ila, Amurka da yin barazanar kai hari kan Iran

A bayyanar shi ta karshe da yayi a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a jiya laraba, Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad, ya zargi kasashen yammaci da kasar Amurka da Isra’ila da yi wa kasarsa barazanar kai mata harin soja. A wannan shekarar dai, babu wani Jami’in kasar Amurka ko na Isra’ila da ya fice daga dakin taron, kamar yadda su ka taba yi a baya.  

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad
Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad Reuters
Talla

Rige - rigen da manyan kasashen duniya ke yi wajen kera makamai da kuma bada tsoro ta hanyar makamansu na Nukliya, da kuma son gwada sabbin makamansu na zamani da suka kera, ya zama wata sabuwar hanyar yiwa kasashen duniya barazana domin tilasta masu mika wuya a garesu.

‘Barazanar da kasar Isra’ila ke ci gaba da yi na yin amfani da karfin soja a kan babbar kasarmu na nuna karara gaskiyar wannan kazamar niya ta kasashen’ ini Ahmadinejad.

Shugaban na Iran yak ara nuni da take - taken da Isra’ila ke ta yi na kokarin kai harin soja kan cibiyoyin Nukliyar kasar Iran.

Tuni dai shugaban kasar Amurka Barack Obama, a gaban taron na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana karara aniyar kasar Amurka cewa kasarsa zata yi duk wani abu da ya dace wajen ganin ta hana kasar Iran mallakar makaman Nukliya, a dai dai lokacin da kasashen turai kuma ke cigaba da nazarin fito da wasu sabbin hanyoyin kakabawa Iran takunkumi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI